An yi fito na fito da 'yan sanda a Hong Kong

Masu zanga zanga a Hong Kong
Image caption Masu zanga zanga a Hong Kong

'Yan sanda a Hong Kong sun yi arangama da masu zanga-zangar neman kafuwar democradiyya wadanda ke kokarin zagaye hedikwatar gwamnati.

'Yan sandan sun yi amfani da barkonon tsohuwa da kulake a yayinda suke tarwatsa masu zanga-zangar wasu daga cikinsu dake jefa ma 'yansandan makamai masu cutarwa.

An cafke a kalla mutane arba'in. Kungiyoyin dalibai sun yi kiran da a kara kaimi a zanga-zangar wadda kawo yanzu ta kai watanni biyu. Suna bukatar a kyale 'yan yankin na Hong Kong ne su zabi Shugabanninsu, ba tare da tsoma bakin hukumomi a Beijing ba.

Karin bayani