Mutane shida sun rasu a harin kasuwar Maiduguri

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Boko Haram ta hallaka dubban mutane a bana

Mutane a kalla shida ne suka rasu sannan wasu kusan hamsin suka jikkata samakon tashin bama-bamai biyu a kasuwar Monday a Maiduguri na jihar Borno.

Bayanai sun ce mata biyu 'yan kunar-bakin wake ne suka fasa bam din a layin 'yan kaji na kasuwar.

A makon da ya wuce ma an kai hari a kasuwar Monday din lamarin da ya janyo mutuwar mutane fiye da 70.

Harin na Maiduguri na zuwa ne kwanaki uku bayan da aka kai hari a Masallacin Juma'a a Kano, inda mutane fiye da 100 suka rasu sannan wasu fiye da 200 suka jikkata.

Ana zargin kungiyar Boko Haram da kaddamar da wadannan hare-haren.