Najeriya ta soke horon da Amurka ke wa dakarunta

Amurka ta nuna takaici dangane da wani mataki da Najeriya ta dauka na yanke dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu ta horar da dakaru a daidai lokacin da Najeriyar ke fama da masu ta-da-kayar-baya.

Wata sanarwar da ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya fitar,ta nuna rashin jin dadin dakatar da wani horon hadin gwiwar da dakarun Najeriya da kuma wasu farar-hula, wadanda a baya ba su da horon Soji domin yaki da kungiyar Boko Haram.

Wasu dai na ganin wannan mataki da Najeriyar ta dauka a matsayin ganganci.