Yunwa na yi wa 'yan Syria barazana

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Matsalar yunwa za ta iya shafar mutane miliyan daya da rabi

Hukumar samar da abinci ta duniya ta ce za ta dakatar da muhimmin shirin samar da tallafin abinci ga 'yan gudun hijirar Syria.

'Yan Syria su fiye da miliyan daya da dubu dari bakwai ne ke zaune a kasashe makwabta.

Hukumar ta ce matsalar karancin kudade ya tilasta mata dakatar da baiwa 'yan gudun hijirar takardun karbar abinci a kantunan abinci a kasashen Jordan da Lebanon da Turkiya da Iraki da kuma Masar.

Tana mai gargadin cewa idan ba'a sami gudunmawar abinci ba, iyalai da dama za su zauna da yunwa a hunturun bana.

Babbar daraktar shirin samar da abincin ta duniya, Ertharin Cousin ta bukaci kasashe masu ba da taimakon jin kai su rubanya ba da tallafin kudi.