An kashe 'yan sanda 33 a Damaturu

Hakkin mallakar hoto google
Image caption Boko Haram ta hallaka jami'an tsaro da dama a Nigeria

Ma'aikatan asibiti a Damaturu babban birnin jihar Yobe sun ce an kai gawawwakin 'yan sanda 33 da kuma na soji shida sakamakon harin 'yan Boko Haram.

Bayanai sun ce an kashe 'yan Boko Haram kusan 20 bayan da suka kaddamar da hari a Damaturu a ranar Litinin inda suka kona babban sansanin 'yan sanda da kuma wasu gine-ginen gwamnati.

A matsayin wani mataki na murkushe ayyukan kungiyar, gwamnatin jihar Yobe ta kafa dokar hana fita ba dare ba rana a daukin birnin Damaturu.

Wani mazaunin Damaturu ya shaida wa BBC cewa an kashe daruruwan mutane a garin sakamakon barin wuta tsakanin dakarun gwamnati da 'yan Boko Haram.

A cikin makon guda, hare-haren 'yan Boko Haram sun janyo mutuwar mutane a kalla 247 a jihohin Kano da Borno da kuma Yobe.