DFID ta horar da 'yan banga a Najeriya

Hakkin mallakar hoto

Hukumar raya kasashen ta Biritaniya DFID ta horar da wasu 'yan kungiyar banga su dari daya a Najeriya kan yadda za su rika bai wa al'umominsu kariya.

An dai bai wa 'yan bangar horon ne kan yadda za su tsara kungiyoyinsu, da gudanar da su, da daukar sabbin membobi da kuma kare hakkin dan'adam.

A baya nan dai 'yan banga na taka muhummiyar rawa wajen bai wa al'ummomin dake fuskantar hare-hare daga mayakan Boko Haram da masu fashin shanu kariya a kasar ta Najeriya.

'Yan banga da mafarauta a Najeriya na taka mahimmiyar rawa wajen yaki da masu tayar da kayar baya musamman a arewa maso gabashin kasar.