Iraki ta cimma yarjejeniya da Kurdawa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A yanzu za a dunga fitar da mai ta yankin Kurdawa

Gwamnatin Iraki ta ce ta cimma yarjejeniya da yankin Kurdawa mai cin gashin kansa game da fitar da mai zuwa kasashen ketare bayan shafe tsawon watanni ana ta zazzafar takaddama.

Yarjejeniyar za ta bada damar safarar man daga yankunan Kurdawa ta hannun babban kamfanin mai na kasar Iraki wanda zai hada da ganga 300,000 na danyen man a kullum daga Kirkuk.

A waje guda kuma fadar gwamnati a Bagadaza za ta saki kason yankin Kurdawan na kudin shiga wanda ta rike fiye da shekara daya yanzu.

Hakan nan kuma za ta bada kason kasafin kudin na fannin tsaro ga mayakan Peshmerga na Kurdawa.

Masu aiko da rahotanni sun ce yarjejeniyar wani matakin cigaba ne na kyautata hadin kai a yakin da ake yi da mayakan kasar muslunci a Iraki.