An damke matar Al Baghdadi a Lebanon

Image caption Shugaban kungiyar IS, Abubakar Al Baghdadi

Jami'an kasar Lebanon sun ce an kama matar shugaban kungiyar kasar musulunci Abubakar al Baghdadi da kuma daya daga cikin 'ya'yansu a kan iyakar Syria.

Jaridar Assafir ta Beirut ta ruwaito cewa tsawon kwanaki kenan ake tsare da su bayan da suka yi kokarin shiga cikin Lebanon da takardun boge.

A halin yanzu ana yi musu tambayoyi a shalkwatar ma'aikatar tsaron kasar.

Jaridar ta ce an yi nasarar kamen ne da hadin gwiwar hukumomin leken asiri na kasashen waje.

'Yan kungiyar kasar musuluncin suna ci gaba da garkuwa da wasu sojojin Lebanon inda suke barazanar hallaka su.