An kori ministan tsaron Kenya

Hakkin mallakar hoto afp
Image caption Kenyatta ya cire shugaban 'yan sandan Kenya

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya sanar da murabus din shugaban 'yan sandan kasar, sakamakon harin da 'yan kungiyar Al shabab suka kai kasar, inda suka kashe wasu masu aikin fasa dutse 36.

Rahotanni dai sun ce an kai wannan harin ne jiya da daddare, inda maharan suka bude musu wuta a kan tantunan da ma'aikatan ke kwance.

Wasu da lamarin ya faru a kan idanunsu dai sun ce sai da maharan suka ware wadanda ba musulmi ba, kana suka yanka wasu, sannan suka harbe sauran.

Shugaba Kenyatta ya bayyana wadanda suka kai harin a matsayin mahaukata.