Zamfara: Matasa sun bankawa caji ofis wuta

Hakkin mallakar hoto zamfara website
Image caption Gwamna Abdulaziz Yari na Zamfara

Rahotanni daga jihar Zamfara a arewacin Nigeria sun ce wani rikici ya barke a karamar hukumar Shinkafi inda wasu gungun mutane suka bankawa ofishin 'yan sanda wuta.

An soma tashin hankali ne saboda mutanen na zargin 'yan sanda da kokarin kokarin sakin wani mutumi mai dauke da makamai wanda aka damke shi a Shinkafi a yayinda 'yan sandan suka tafi da shi zuwa Gusau.

Wani mazaunin garin Shinkafi ya shaida wa BBC cewa "An harbi mutane uku sakamakon rikicin, sannan mutane sun koma gida, an rufe shaguna."

Kakakin 'yan sandan jihar Zamfara ya ce an baza jami'an tsaro a garin Shinkafin domin kwantar da tarzomar.

Bayanai sun ce yanzu haka kurar tashin ta lafa