Twitter na aiwatar da wasu canje- canje

Hakkin mallakar hoto Getty

Shafin sada zumunta na Twitter na aiwatar da wasu canje- canje da nufin bai wa masu amfani da shafin damar bada rahotan duk wani cin zarafi da aka sanya cikin sauki

Canje- canjen na zuwa ne bayan an ci zarafin wasu fitattun mutane a shafin.

Wata jami'ar shafin Twitter mai kula da manufofin da suka shafi jama'a a Turai Sinead McSweeney, ta ce 'mun sha fadin cewa tsaron lafiyar masu amfani da shafin twitter shine abu mai mahimmanci'.

'Wani aiki ne da bamu taba daukar cewa an kammala shi ba' in ji ma'aikaciyar shafin na Twitter.

Shafin sada zumuntar na Twitter ya ce za a soma aiwatar da canje- canjen a 'yan makonni masu zuwa.

Masu amfani da Twitter za kuma su iya bada rahotan cin zarafi wanda ba kai tsaye aka yi domin su ba