Tasirin sauyin yanayi da karuwar al'uma

Climate Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Karuwar al'uma za ta iya haifar da matsananci yanayi ga mutane

Wata kungiya mai suna Royal Society ta ce sauyin yanayi da karuwar al'uma za su kara haifar da matsanancin yanayi ga mutane.

A wani rahoto da kungiyar ta fitar, ta ce ci gaba da yin amfani da ababan dake kara dumamar yanayi akan al'umar da ta mafi yawanta suka manyanta zai karu da kashi kusan goma nan da shekarar 2090.

Haka a cewar rahoton hakan zai iya haifar da karuwar ambaliyar ruwa da kashi hudu da kuma matsalar fari.

"Wannan ba damuwa ce da ake tunanin za ta auku ba, tuni lamarin ma ya fara aukuwa." In ji Farfesa Goergina Mace, wandda ta jagoranci rubuta rahoton.

Ta kara da cewa akwai bukatar a mutane su canja tunani da tsare tsare akan abubuwna da suka shafi canjin yanayi da karuwar al'uma.

Rahoton ya kara da cewa, gwamnatoci da dama ba su fahimci hadarin dake tattare da hakan ba yayin da garuruwan dake gabar teku ke ci gaba fuskantar barazanar amabilyar ruwa.

"Haka kuma mutane suna zama a inda bai dace ba a wuraren dake tattare da hadari." Farfesa Mace ta kara da cewa.

Ta kara da cewa zai yi wuya a kaucewa faruwar haddura amma kuma ba zai zamanto abu mai wuya ba idan ana so a zauna a cikin shiri.