APC ta tantance 'yan takarar shugaban kasa

Image caption Jam'iyyar APC za ta fuskanci kalubale daga PDP mai mulkin kasar

Jam'iyyar APC mai adawa a Nigeria ta tantance mutane biyar da ke neman tikitin tsayawa takarar shugabancin kasar a zaben 2015.

'Yan takarar da aka tantance su ne; Janar Muhammadu Buhari da Alhaji Atiku Abubakar da Gwamna Rabiu Kwankwaso da Gwamna Rochas Okorocha da kuma Mr Sam Nda-Isaiah.

Shugaban kwamitin tantance 'yan takarar, Ogbonnaya Onu ya ce jam'iyyar za ta bai wa kowanne dan takara dama domin kawo sauyi a Nigeria.

Jam'iyyar APC ta tsayar da ranar 10 ga watan Disamba domin zaben fitar da gwani tsakanin 'yan takarar biyar da za a gudanar a jihar Edo.

Masu sharhi na ganin cewar takarar za ta fi zafi tsakanin Janar Buhari da Atiku Abubakar wadanda ake gani sun fi sauran 'yan takarar magoya baya.