Yara sun shaku da kwamfuta a Biritaniya

Bincike ya nuna cewa dalibai na amfani da kwamfutocin tafi da gidanka a kusan kashi 70% na makarantun Firamare a Biritaniya.

Amma binciken ya ce babu wata hujja karara dake nuna cewa hazakar daliban wajen karatu ta karu ta hanyar amfani da kwamfutocin tafi da gidanka.

Binciken ya kuma yi nazari ne akan makarantun gwamnati guda 671 da kuma wasu makarantu masu zaman kansu

Dalibai da dama sun bada rahotan cewa su kan dauki kwamfutar su mai hade da internet har zuwa wajen kwanciya domin ci gaba da shiga shafukan musayar ra'ayi da muhawara domin hira.

Bincike ya nuna a yanzu ana amfani da kwamfutocin hannu akalla a cikin kashi 68% na makarantun firamare da kuma makarantun gaba da firamare kashi 69%

Amma masu binciken sun gano cewa a kashi 9% na makarantun, kowanne dalibi na da na'urar kwamfutarsa.

Tsakanin shekarar 2014 da 2016, ana tsammanin yawan kwamfutocin hannu a makarantu zai karu daga kusan 430,000 zuwa kusan 900,000

Binciken ya kuma nuna cewa a gidaje masara karfi akwai yiwuwar yara zasu rinka karatunsu ne akan kwamfuta a madadin litattafai

I