Za a gwada mota mara matuki a yankunan Burtaniya

Britain Driverless
Image caption Za a gudanar da gwajin ne a yankuna hudu na Burtaniya

Burtaniya ta fitar da sunayen yankuna hudu da za a fara gwada yin amfani da mota mara matuki.

Yankunan sun hada da Greenwich dake kudu maso gabashin London da Bristol da Conventry da kuma Milton Keynes.

Wannan mataki da aka dauka an bayyana shi ne a wata sanarwa da kamfanin quango a Burtaniya ya fitar.

A yankin Bristol, gwajin motar wanda kungiyar Axa za ta dauki nauyi zai mayar da hankali ne wajen ganin ko za a iya rage cunkoson ababan hawa.

Mambobin wannan yanki za kuma su kula da irin yadda mutane za su karbi wannan nau'in motoci tare da abin da ya shafi shari'a da kuma batun inshora.

A yankin Greenwich kuwa wanda anan ne ginshikin gwajin motar ya ke hukumar dake kula da bincike akan motoci da kuma kamfanin General Motors da na AA da RAC ne za a su jagoranci gwajin.

Wanna bagaren zai mayar da hankali ne kan daukan fasinjojin haya da kuma yadda za a dinga ajiye motocin.

Yankunan Milton Keynes da Coventry kuma za su dauki nauyin jagorantar shirin na ababan hawa masu sarrafa kansu baki daya.