Ebola: 'Yan Najeriya sun tafi bada taimako

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Har yanzu akwai jan aiki a gaba wajen yaki da cutar

Wasu jami'an lafiya su sama da 200 'yan Nigeria na kan hanyarsu ta zuwa yankin da cutar ebola ke yaduwa, domin bada irin nasu taimakon.

Ana tsammanin rukunin farko na jami'an kiwon lafiyar za su isa Saliyo ranar Alhamis ko Jumu'a karkashin jagorancin kungiyar Likitoci ta Medecins Sans Frontiers

An dai yi wa jami'an lafiyar bikin ban-kwana a birnin Legos.

Kuma galibinsu sun nuna kwaringwiwar cewa tafiyar su zata yi amfani wajen yaki da cutar.

Koda yake kasashe masu arziki da kuma wasu manyan kungiyoyin bayarda agaji na bada tasu irin gudummuwar, duk da haka su ma 'yan Afirka suna da muhimmiyar rawar da za su taka wajen yaki da cutar.

Tuni dai aka shawo kan cutar ebola a Nigeriar.