Boko Haram: Al'ummar Kano na azumi

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sarki Muhammadu Sanusi na biyu ya ce babu wanda ya isa ya hana Kanawa bauwata Allah

A yau Laraba ne al'ummar jihar Kano ke fara azumi na musamman kwanaki uku domin rokon Allah ya magance matsalolin rashin tsaron da ke addabar jihar.

A makon jiya ne dai mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu ya bukaci mazauna jihar su yi azumin bayan 'yan bindigar da ake zaton 'yan Boko Haram ne sun kai hari a babban masallacin Juma'a da ke kusa da fadarsa.

Harin dai ya yi sanadiyar mutuwar fiye da mutane dari daya.

Sarki Muhammadu Sanusi na biyu ya ce babu wani dan ta'adda da ya isa ya hana Kanawa bautawa Allah, don haka harin ba zai razana su ba.

Za a yi azumin ne daga Laraba zuwa ranar Juma'a.