Duniya tana fuskantar mummunar dumamar yanayi

Dumamar yanayi Hakkin mallakar hoto PA

Hukumar kula da yanayi ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi kashedin cewa duniya ta kama hanyar fuskantar dumamar yanayi mafi girma a bana irin wadda ba a taba gani ba.

Hukumar ta ce hakan na tabbatar da karuwa ba kakkautawa da ake samu na sauyin yanayi.

Mukaddashin babban sakataren kungiyar nazarin yanayi ta Majalisar Duniya, Jeremiah Lengoasa ya karin haske:

"Idan aka kwatanta watannin Janairu zuwa Oktoban 2014 da shekarun baya.

Idan watanin Nuwamba da Disamba suka kasance a kan irin wannan dumamar da ba a saba gani ba, to kuwa hasashen da za a iya yi ga shekarar ta 2014 a kan wannan ma'auni zai sanya shekarar zama mafi zafi a tsawon tarihi.