Sojoji sun yi galaba kan Boko Haram a Konduga

Image caption An shafe shekaru biyar ana yaki tsakanin dakarun Nigeria da 'yan Boko Haram

Rundunar sojin Nigeria ta yi nasarar lalata wata motar 'yan Boko Haram makare da abubuwan fashewa a garin Konduga na jihar Borno.

Wata majiyar jami'an sojin ta shaida wa BBC cewa 'yan Boko Haram na shirin kaddamar da ayyukan ta'addanci ne a Kondungan kafin a katse hanzarinsu.

Hakan na zuwa ne bayan da sojojin suka hallaka 'yan Boko Haram kusan 70 a Kondunga a ranar Talata lokacin da 'yan kungiyar suka kai hari kan jami'an tsaro.

Bayanai sun nuna cewar a cikin 'yan kwanakin nan jami'an tsaron Nigeria na samun galaba a kan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar.

Ko a ranar Litinin, sojoji sun kashe 'yan Boko Haram kusan 100 a Damaturu babban birnin jihar Yobe a wata ba ta kashi da suka yi.