Diffa: An kafa dokar takaita zirga zirga

Hakkin mallakar hoto

A Jamhuriyar Nijar, hukumomin jahar Difa mai iyaka da jahohin Yobe da Borno masu fama da matsalar boko haram,sun kafa dokar takaita zirga zirgar motoci da babura daga karfe 8 na dare zuwa karfe 6 na safe.

Hukumomin sun ce an sanya dokar ce saboda dalilai na tsaro,sakamakon hare haren da 'yan kungiyar boko haram ke dada kaiwa a wasu garuruwan Najeriya masu iyaka da jahar ta Difa.

Sai dai gwamnan jahar ta Difa malam Yakubu Sumana Gawo ya fada wa BBC cewa dokar bata shafi masu tafiya a kasa ba ko kuma akan dabbobi.

Akwai 'yan gudun hijirar da suka tserewa rikicin Boko Haram da yawa a garin Diffa.