'Akwai tulin mata 'yan kunar bakin wake a Borno'

Image caption 'Yan Boko Haram na tafka ta'asa a Nigeria

Wata majiyar tsaro ta shaida wa BBC cewar akwai tarin mata 'yan kunar bakin wake da ke yunkurin kaddamar da hare-hare a jihar Borno.

Jami'in sojin ya bayyana cewar matan 'yan kunar bakin wake sun bullo da wasu dabaru na aikata ta'addanci a jihar sai dai sojoji sun gano kuma suna dakile yunkurin.

Majiyar ta ce an damke wata 'yar kunar bakin wake a Konduga kafin ta tada bam din a ranar Laraba.

A cikin 'yan watannin nan mata 'yan kunar bakin wake sun kai hare-hare a sassa daban-daban a kasar musamman a Maiduguri.

Rikicin Boko Haram ya janyo mutuwar mutane fiye da 10,000 a Nigeria.

Haka kuma mutane fiye da miliyan daya da rabi sun rasa muhallansu sakamakon tashin hankali.