Kenya: An gano matattarar masu laifuka a intanet

Kenya
Image caption Ana bincike domin a gano ko mutanen 'yan asalin kasar kenya ne

'Yan sandan kasar Kenya sun gano wani wuri da ake aikata laifuka a shafin intanet.

A cewar 'yan sandan wasu 'yan kasar China su 77 ne suke kula da wurin wanda yake Nairobi babban birnin kasar.

Daga cikin laifukan da ake zargin suna aikatawa akwai yin kutse a shufakan intanet da kuma ajiye kudade a kasashen waje ba bisa ka'ida ba.

Bayanai na kuma nuna cewa yanzu haka an tsare mutanen na tsawon kwanaki biyar ana gudanar da bincike.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Kenya ta gayyaci wani jami'in diplomasiyyar kasar China domin ta tattauna da shi game da batun.

Wani jami'in kasar China har ila yau ya ce ofishin jakadancin China na taimakwa wajen gudanar da binciken.

Rahotanni sun kuma ce ana duba fasfo din mutanen domin a tabbatar da ko 'yan asalin kasar China ne kamar yadda suka nuna.

Har ila yau za a tuhumi mutanen akan laifin shiga kasar ta Kenya ba bisa ka'ida ba.