PDP ta dakatar da Bamanga Tukur

An dakatar da Bamanga har tsawon wata daya
Bayanan hoto,

An dakatar da Bamanga har tsawon wata daya

Jami'iyyar PDP mai mulkin Najeriya ta dakatar da tsohon shugabanta, Alhaji Bamanga Tukur saboda ya je kotu yana neman a cire shugaban jam'iyyar daga karagar mulki.

A wata sanarwa da jam'iyyar ta fitar, ta ce Alhaji Bamanga Tukur zai kuma gurfana a gaban kwamitin ladabtarwarta domin yin bayani kan dalilan da suka sanya ya kai ta kara kotu.

Kazalika, jam'iyyar ta ce ba ta ji dadin yadda tsohon shugaban nata ya tsallake hanyoyin da ta shimfida na yin sulhu , ya ta fi gaban kuliya.

A yanzu dai jam'iyyar ta PDP ta ce Alhaji Bamganta Tukur zai karbi horon dakatarwa har tsawon wata daya kafin ta duba lamarinsa.

A kwanakin baya ne dai wani na haunnu-damar Alhaji Bamanga mai suna Aliyu Abuba Gurin ya kai shugaban jam'iyyar, Amadu Mu'azu kara, yana mai bukatar kotu ta cire shi, kana ta mayar da Bamanga Tukur saboda, a cewarsa wa'adinsa bai kare ba lokacin da ya sauka daga shugabancin jam'iyyar.