Shugaba Putin ya zargi kasashen yamma

Vladimir Putin Hakkin mallakar hoto AP

Shugaba Putin ya zargi kasashen yamma da yunkurin yi wa kasar Rasha zagon kasa, ya ce suna amfani da rikicin da ke faruwa a kasar Ukraine a matsayin madogarar kakaba wa kasar tasa takunkumi.

A wani jawabinsa na shekara ga kasa, Mr Putin ya kuma kare matsayin hadewar kasar Rashar da yankin Crimea, da kuma matakin da ta dauka a gabashin Ukraine.

Ya kuma zargi wadanda ya kira 'yan ba-ni-na-iya a kan matsin tattalin arzikin da kasar ta shiga.

Amurka dai ta yi watsi da zargin, inda sakataren harkokin wajen kasar John Kerry, ya ce kasashen duniya ba suna neman yin fito-na-fito ba ne.

Ya kuma ce Rashar za ta iya dawo da martabarta idan ta daina mara baya ga mayaka 'yan a-ware na gabashin Ukraine.