ICC: An janye karar Shugaba Kenyatta

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaba Kenyatta a lokacin da ya gurfana gaban ICC

An janye karar da ake tuhumar shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta wanda aka gabatar gaban kotun duniya mai shari'ar manyan laifuka.

Masu gabatar da karar sun shigar da takardar bukatar janye tuhumar bayan da alkalai suka ki basu wani karin lokaci na tattara bayanai.

Ofisihin masu gabatar da karar ya ce gwamnatin kasar Kenyar taki ta mika cikakkun shaidu.

An tuhumi mi Kenyatta ne da hannu a tarzomar da ta barke bayan zaben da aka gudanar na shugaban kasa a shekarar 2007.

Mutane fiye da dubu daya ne suka rasa rayukan su a tarzomar.

Sai dai kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Right Watch ta ce ,matakin wani koma baya ne ga yunkurin da ake na kawo karshen cin zarafin bil adama a kasar ta Kenya.