Shekara guda da rasuwar Nelson Mandela

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mutane na ci gaba da jimamin Mandela a duniya

Al'ummar Afrika ta Kudu na bukin tuna wa da margayi Nelson Mandela wanda shekara guda kenan da rasuwarsa.

Tsofaffin 'yan gwagwarmayar yaki da mulkin danniya na fararta sun halarci bukin da aka yi a birnin Pretoria.

Matar da Mandela ya bari, Graca Machel ita ma ta halarci bukin inda ta saka furrani a karkashin butunbutumin tsohon shugaban kasar.

An busa algaitar vuvuzela kafin a yi shiru na mintuna uku domin jimamin mutuwar Nelson Mandela.

A hirarta da BBC, jikar Mandela, Ndileka Mandela ta ce 'yan Afrika ta Kudu na ci gaba da rike abubuwan da Mandela ya bari a kasar kan zaman lafiya da yafe wa juna.

Nelson Mandela, mai yakin neman 'yancin bakaken fata, shi ne zababben shugaban kasa karkashin mulkin demokradiya na farko a Afrika ta Kudu.