'Yan bindiga sun fasa gidan yari a Minna

Hakkin mallakar hoto AFP

Rahotanni daga Minna, babban birnin Jihar Niger da ke tsakiyar Najeriya sun ce wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun balle kofar sabon gidan kurkuku da ke Tunga, a birnin na Minna, inda suka kubutar da wasu da ake tsare da su.

A cewar rahotannin, ba a rasa rai ba a lamarin, amma wasu daga cikin ma'aikatan gidan yarin sun samu raunuka a arangamar da suka yi da 'yan bindigan.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Niger, DSP Ibrahim Gambari ya tabbatar da faruwar lamarin, amma bai fayyace ko fursunoni nawa ne suka tsere ba.

Sai dai ya ce jami'ansu sun samu nasarar sake cafke mutane 12 da ake zargi suna daga cikin fursinonin da suka tsere.

Rahotanni sun ce kimanin fursinoni 270 ne a gidan yarin, lokacin da aka kai harin, kuma guda 53 ne suka rage.