Biritaniya za ta kafa sansanin soji a Bahrain

Hakkin mallakar hoto GETTY IMAGES
Image caption Wasu na ganin Bahrain na neman kariya ne daga mayakan IS

Burtaniya da Bahrain sun amince da wani shiri na kafa wani sasanin sojin -ruwa a kasar ta Bahrain.

Sansanin sojin na Burtaniya zai kasance shine na farko a yankin Gabas ta Tsakiya , tun bayan janyewar dakarun kasar a yankin a shekarar 1971.

Sakataren tsaron kasar Burtaniya, Michael Fallon, ya ce dakarun da za jibge a yankin, za su taimaka wajen samar da zaman lafiya, musamman ma a daidai wannan lokaci da ake fuskantar barazanar mayakan IS.

Sai dai bayanai na nuna cewa mai yuwuwa, shirin ya samu suka daga wani bangare, idan aka yi la'akkari da tarihin kasar ta Bahrain a fannin kula da hakkokin bil adama.