Mahaukaciyar guguwa na dosar Philippines

Hakkin mallakar hoto EPA

A kasar Philippines, miliyoyin mutane na fake a makarantu da coci-coci da kuma wasu dakuna da aka gina na wucin- gadi, yayin da wata mahaukaiyar guguwa da ake kira "Hagupit" ta doshi kasar.

Fiye da mutane rabin miliyan ne suka kauracewa gidajensu dake bakin Gabar Teku, yayin da ake dakon isowar guguwar nan da wani lokaci kadan.

Bayanai sun ce guguwar ta doshi yankunan Gabashi da Arewacin biranen Samar da kuma Tacloban, inda dubban mutane suka rasa rayukansu a a bara bayan da guguwar Haiyan ta abkawa yankin.

Wani jami'in kasar Philippines ya ce a wannan karo an kwashe dubban mutane zuwa wasu cibiyoyo da aka tanada, sai dai babban abin da muke tsaro shine guguwar za ta shafi yankunan da guguwar Haiyan ta daidaita a baya."