'Hukuncin kisa kan 'yan ta'adda a Kamaru'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun Kamaru na jiran ko-ta-kwana

'Yan majalisar dattijai a Kamaru sun amince da kudurin dokar da ya tanadi hukuncin kisa kan wanda aka kama da hannu a ta'addanci a kasar.

A yanzu kudurin dokar na jiran sa hannun Shugaba Paul Biya.

'Yan adawa a kasar Kamaru sun zargi gwamnati da yunkurin amfani da dokar domin murkushe masu kin mulkin shugaba Biya da ya shafe shekaru 32 a kan mulki.

Kungiyar Boko Haram na kai hare-hare a cikin kasar Kamaru musamman a lardin arewa mai nisa a cikin 'yan watannin nan.

Kungiyar Amnesty International ta ce rabon da Kamaru ta aiwatar da hukuncin kisa tun shekarar 1997.