An samu Jami'an Gambiya da zamba

Ginin Ofishin Jakadancin kasar Gambia a London Hakkin mallakar hoto AP

Wata kotu a London ta samu wasu jami'an diplomasiyyar kasar Gambia da laifin zamba, bayan da suka rika sayar da taba sigari a ofishin jakadancin kasar dake London ta hanyar kin biyan harajin da ya kai kusan fam miliyan hudu da dubu dari takwas.

Mukaddashin shugaban ofishin jadancin Gambia dake Kensington, Yusupha Bojang, da wasu abokan aikinsa sun sayo ton 29 na taba sigari cikin shekaru uku, kuma suna sayowa ne da sunan za a yi amfani da ita a ofishin, don haka sai ana dauke musu biyan haraji a kanta.

An ce Sun ci riba sosai a harkar ta hanyar zille wa biyan harajin da ya kai dala miliyon takwas.

Gwamnatin Gambia ce ta cire wa hudu daga cikin jam'ian nata rigar-kariya, domin a samu damar gurfanar da su gaban kuliya.