Hama ya zama Shugaban jam'iyyar Lumana

Hama Amadou
Image caption Hama Amadou

A Jamhuriyar Nijar, magoya bayan jam'iyar Moden Lumana Afrika, na ci gaba da tsokaci dangane da zaben Malam Hama Amadu a matsayin shugaban jam'iyyar.

Daukacin jahohin kasar ne suka tsayar da takararsa a taron Congres da jam'iyyar ta gudanar jiya lahadi a Yamai.

Shi dai Hama Amadun dai na gudun hijira ne a kasar Faransa tun cikin watan Agustan da ya gabata sakamakon tuhumar da hukumomin na Nijar ke yi masa na cewa yana da hannu a cikin badakalar cinikin jarirai daga Najeriya zuwa kasar ta Nijar, abin da Hama Amadun da magoya bayansa su ka ce bi ta da kullin siyasa ne kawai.

Karin bayani