Jirgin da aka tsare a Kano, ya tashi

Hakkin mallakar hoto Yusuf Yakasai
Image caption Tun a ranar Asabar Nigeria ta kama jirgin saman

Jirgin kayan da aka tsare a birnin Kano na Najeriya shaƙe da makamai wanda kasar Rasha ta ce nata ne, ya tashi.

Wannan ya biyo bayan sakin da tun farko hukumomin Najeriyar suka yi wa jirgin bayan da suka gamsu da bayanan da kasashen Faransa da Rashar suka yi masu

Ofishin jakadancin Faransa a Nigeria ya ce wasu jirage masu saukar-ungulu biyu da ke cikin jirgin nata ne, kuma an dauko su ne daga Jumhuriyar Afirka ta tsakiya da nufin kaiwa kasar Chadi don tallafawa ga yakin da ake yi da masu ta-da-kayar-baya.

A cewar Faransa an karya linzamin jirgin zuwa Najeriya ne saboda cinkoson a filin saukar jiragen sama na kasar Chadin.

Hakkin mallakar hoto Yusuf Yakasai
Image caption Faransa ta ce makaman nata ne

Mahukunta a Najeriya sun ce, sun gunadar da bincike, yayin da wasu matasa suka yi cincirindo a filin saukar jiragen sama na Aminu kanon, suna kira da a tabbatar da adalci wajen binciken.

Kamun da aka yi wa jirgin dai ya jawo zaman dar-dar a Kano, inda mutane ke zargin yana dauke ne da irin makaman da ake yin amfani da su wajen tayar da hankali a Najeriya.

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba