Aliyu, Jang, Dakingari sun lashe zaben PDP

Image caption Wasu jiga jigan jam'iyyar ta PDP ba su kai labari ba

Gwamnoni hudu na jam'iyyar PDP wadanda wa'adin mulkinsu zai kare a shekarar 2015 sun lashe zaben fitar da gwani na kujerun 'yan majalisar dattawan kasar.

Gwamna Mu'azu Banbangida Aliyu na Naija da Jonah Jang na Plateau da Sa'idu Dakingari na Kebbi da Gabriel Suswam na Benue sun lashe zabukan fitar da gwanin da jam'iyarsu ta gudanar a karshen makon jiya.

Su ma wasu jiga-jigan jam'iyyar ta PDP sun lashe zaben fitar da gwanin, cikinsu har da shugaban majalisar dattawan kasar, David Mark da mataimakinsa, Ike Ikweremadu.

Sai dai wasu fitattun 'yan majalisar dattawan sun gaza kai batansu a zaben fitar da gwanin , cikinsu har da: Nenadi Usman da Victor Ndoma Egba.

Kazalika, gwamnonin da suka janye aniyarsu ta tsayawa takarar majalisar dattawan sun hada da gwamna Sullivan Chime na Enugu da Emmanuel Uduaghan na Delta da kuma Martis Elechi na Ebonyi.