An saki jirgin da aka kama a Kano

Hakkin mallakar hoto RIA Novosti
Image caption Kamun da aka yi wa jirgin a Kano dai ya jawo zaman dar-dar

Rahotanni daga Najeriya na cewa hukumomin kasar sun saki jirgin saman da aka kama a Kano a karshen makon jiya dauke da makamai.

Rahotannin na cewa an saki jirgin saman ne bayan an gudanar da bincike mai zurfi.

Wani kamfanin dillancin labaran Rasha ya ce jirgin na dakon kaya ne da ke dauke da makaman da za a kai wa dakarun kiyaye zaman lafiyar Faransa da ke aiki a kasar Chadi.

Kamfanin dillancin labaran ya ce jirgin bai samu wurin sauka a Chadi ba ne shi ya sa ya sauka a filin jirgin saman Kano.

Kamun da aka yi wa jirgin dai ya jawo zaman dar-dar a Kano, inda mutane ke zargin yana dauke ne da irin makaman da ake yin amfani da su wajen tayar da hankali a Najeriya.