Ba a saki jirgin da aka kama a Kano ba

Hakkin mallakar hoto RIA Novosti
Image caption Kungiyoyin matasa sun fara zaman-dirshan domin ganin an gudanar da bincike kan jirgin

BBC ta tabbatar da cewa ba a saki jirgin da aka kama dauke da makamai a Kano ba, sabanin rahotannin da wasu kamfanonin dillancin labarai suka bayar cewa an sake shi.

Wakilin BBC a Kano ya ce har yanzu jirgin yana nan a tsare.

Kazalika, wakilin namu ya ce wasu kungiyoyin matasa na Kano sun fara wani zaman dirshan a filin saukar jiragen saman na Kano domin matsin lamba ga hukumomi don a gudanar da cikakken bincike game da jirgin.

A ranar Asabar ne dai jirgin na kasar Rasha dauke da makamai ya sauka a filin jirgin saman malam Aminu Kano, kuma da saukarsa hukumomi suka tsare shi bayan an tabbatar yana dauke da makamai.

Wani kamfanin dillancin labaran Rasha ya ce jirgin na dakon kaya ne da ke dauke da makaman da za a kai wa dakarun kiyaye zaman lafiyar Faransa da ke aiki a kasar Chadi.

Kamun da aka yi wa jirgin dai ya jawo zaman dar-dar a Kano, inda mutane ke zargin yana dauke ne da irin makaman da ake yin amfani da su wajen tayar da hankali a Najeriya.