Kotun Afrika ta Kudu ta wanke Dewani

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shrien Dewani da Anni

Wata mai shari'a a Afrika ta Kudu ta yi watsi da karar da aka shigar kan Shrien Dewani, dan kasuwan nan dan Birtaniya da ake zargi da hayar wasu 'yan ina-da-kisa, suka kashe matarsa Anni, lokacin da suka je yawon cin amarci a birnin Cape Town.

Mai shari'a Jeanette Traverso, ta wanke Mr Dewani daga aikata laifin tana mai cewa masu gabatar da kara sun gaza bayar da kwararan shaidu da zasu sa a same shi da laifi.

Haka nan ta yi watsi da bahasin da babbar shaidar masu gabatar da kara suka gabatar, wani direban tasi, wanda yanzu haka aka daure kan laifin aikata kisan shi da wasu abokansa.

Sai dai bangaren dangin Amaryar da aka halaka sun ce hukuncin bai musu dadi ba.