Chadi ta musanta masaniya kan jirgin Rasha

Image caption Ana zargin akwatunan da ke jirgin na dauke da makamai ne

Jakadan kasar Chadi a Nigeria, Issa Brahim ya ce ya yi mamakin sanya sunan Chadi a cikin maganar jirgin Rasha da aka kama a Kano.

A wata hira da BBC, jakadan ya ce Rasha ta amince jirgin kayanta ne, yayin da Faransa ta amince cewa kayan da ke cikin jirgin jirage biyu masu saukar ungulu da wasu kwatuna a rufe nata ne.

Mr. Brahim ya kuma nisanta kasarsa da korafe-korafen da ake na cewa tana da hannu a rikicin Boko Haram a Najeriya.

Bayanai sun nuna cewa jirgin na kan hanyarsa ne ta zuwa Chadi, amma ya sauka a filin jiragen sama na Malam Aminu saboda cunkoso a filin jiragen saman na Chadi.