'Yan Habasha 70 sun nutse a Bahar Maliya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kimanin mutane 200 suka hallak a Bahar Maliya a wannan shekarar a cewar hukumar 'yan gudun hijira

Wani jirgin ruwa dauke da bakin haure 'yan asalin Afrika ya kife a Tekun Bahar Maliya ta bangaren yammacin kasar Yemen, a cewar jami'an kasar.

Kimanin 'yan kasar Habasha 70 da ke jirgin ne suka mutu, bayan iska mai karfi da kuma igiyar ruwa sun kifar da jirgin a tashar jiragen ruwa na Al-Makha.

Dubban 'yan gudun hijira ne ke ratsawa ta Yemen domin tsallaka Bahar Maliya, a cikin jiragen ruwa marasa kwari ga kuma cunkoso a duk shekara.

Daruruwa daga cikinsu ne ke mutuwa a yayin wannan tafiyar zuwa Gabas ta Tsakiya ko nahiyar Turai.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hanyar na cike da hadari

Lamarin na baya-bayanan ya auku ne a ranar Asabar, amma kuma sai a ranar Lahadi aka samu bayanai.

'Yan ci-rani na neman ingantacciyar rayuwa a kasashe kamar Saudi Arabia abinda ke sa su shiga wannan balaguro mai cike da hadari.

A watan Oktoba, hukumar 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya ta ce mutane fiye da 200 sun mutu a cikin teku a bana a kokarinsu na tsallakawa zuwa Yemen.