Amfani da jirgi mara matuki ya ci tura

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Cikin mintina 30 Amazon zai rika aikawa da kayan da aka saya ta jirgin

Kamfanin sayar da kaya ta intanet Amazon, ya ce zai gudanar da karin bincikensa na amfani da jirgi mara matuki wajen kai kaya a wajen Amurka saboda tsauraran dokoki.

Kamfanin yana bincike ne kan yadda zai rika amfani da kananan jiragen marassa matuka wajen aikewa da sakonnin kayan da aka saya ga jama'a.

Tun watan Yuli kamfanin na Amurka yake jiran izinin hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Amurka domin gwada jiragen a kusa da birnin Seattle.

A watan Disamba na 2013 ne kamfanin ya gabatar da shirinsa na aikewa da sakon kayan wanda ya kira Amazon Prime Air.

Mataimakin shugaban yada labarai na kamfanin Paul Misener, ya ce, rashin samun izinin gwajin jiragen zai tilasta musu fita zuwa waje.

Karkashin tsarin aikewa da kayan ta kananan jiragen, mutane za su rika samun kayan da suka saya cikin minti talatin.

Hakkin mallakar hoto AP

Amurka ta ba da izinin jarraba amfani da kananan jiragen marassa matuka a harkar kasuwanci ga kamfanoni shida, ban da Amazon.

Wadanda suka yi nasarasun hada daJami'ar Alaska da hukumra filin jirgin sama na Griffiss a New York da kuma sashen kasuwanci na Dakota.

Kamfanin Amazon yana da wurin jarraba amfani da kananan jiragen a Cambridgeda ke Birtania.

Kamfanin Google da na aikewa da sakonni na DHL su ma suna duba yuwuwar amfani da jirgin maras matuki wajen aike wa da sakonni.

A watan Satumba Google ya jarraba amfani da jirgin, yayin da DHL ya fara aikawa da sako ta jirgin zuwa wani tsibiri a arewacin Turai.