Fasahar neman taimakon gaggawa a sabbin motoci

Motocin bayar da agaji Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Motocin bayar da agaji

Wani sabon tsari na neman taimakon gaggawa ga dukkan sabbin motocin da za su fito daga yanzu zuwa shekara ta 2018.

Za a sanya wani sabon tsari na kiran neman taimakon gaggawa da aka yi ma lakani da ecall ga dukkan sabbin motoci da za a kera daga watan Maris na shekara ta 2018 a karkashin wata yarjejeniya da aka cimma a majalisar dokoki ta Tarayyar Turai.

Wannan sabon tsari zai aike da kiran neman taimakon gaggawa ga hukumomin dake bayar da taimakon na gaggawa idan wani hadari ya afku.

Bincike ya nuna cewar tilasta amfani da tsarin zai taimaka wajen rage tsawon lokacin da a yi ana neman taimakon na gaggawa musamman a yankunan karkara.

To amma wani kwararre ya nemi bahasi a kan abinda za a dauki dogon lokaci kafin a aiwatar da tsarin.

Tun a shekara ta 2012 aka bayar da shawarar bullo da tsarin, amma aka jinkirta shi saboda dalilai da dama da suka hada da damuwa da sirrna mutane.

Masu sukar lamirin shirin ba su da tabbas a kan bukatar samar da tsarin da za a sanya a cikin mota wanda zai iya gano wirinda wata motar take.

A karkashin sabuwar yarjejeniyar, tsarin na ecall zai bayar da bayanai ne kawai da suka shafi:

yanayin motar, da man da take amfani da shi, da lokacin da hadarin ya afku da wurin da ya afke.

Antonio Avenoso, babban darakta na hukumar kare hadurra ta Tarayyar Turai ya yi marhabin da wannan tsari. Yace, "kai agajin gaggawa a wurin da hadari ya afku yana da muhimmanci wajen kare hasarar rayukka. Don haka wannan fasaha za ta taimaka wajen ceton rayukka."

Karin bayani