Kenya na tuhumar Al Jazeera

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tashar ta yi rahoto ne na musamman wanda ya harzuka gwamnatin Kenyan

Kenya ta bayar da umarnin gudanar da bincike a kan tashar talabijin ta Al Jazeera da kuma tuhumar ta da laifi idan ta kama, akan wani rahoto da tashar ta yi da ke zargin 'yan sandan kasar na da wata runduna ta kisan mutane.

Gidan talabijin din na Al Jazeera ya tattauna da wasu mutane da suka ce su jami'an tsaro ne da ke aikin yaki da ta'addanci, kuma suna harar masu tsattsauran kishin Islama ne, bisa umarnin hukumomin kasar.

Gwamnatin Kenyan ta bayyana rahoton a matsayin abin kunya wanda kuma ya saba wa ka'idar aikin jarida, tana mai jaddada cewa ba ta da wannan runduna.

Masu rajin kare hakkin dan adam, daman sun yi zargin cewa, 'yan sanda na kashe malaman addinin Musulunci a birnin Mombasa, mai tashar jirgin ruwa.