Zaben fid da gwani na PDP ya bar baya da kura

Zaben PDP Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Zaben PDP

Yayinda a ranar Litinin jam'iyyar PDP mai mulkin Nijeriya ta gudanar da zabukan ta na fitar da gwanayen ta na takarar gwamna a jihohin kasar domin manyan zabukan kasa baki daya da ake shirin yi a watan Faburairu, rahotanni na cewa lamarin ya gamu da tarin matsaloli a jihohi da dama.

Kusan babu wata jiha da ba a samu tangarda ba, kuma kusan duk suna kukan tilasta bin wani dan takara.

A jihar Katsina ma an tarar da wadannan matsaloli, wadanda har suka sanya sauran 'yan takarar gwamnan a zaben fidda gwanin suka fice cikin fushi daga dandalin zaben.

Cikin 'yan takarar dai har da tsohon mataimakin Marigayi Umaru Musa 'yar adaua a lokacin yana gwamnan Katsina.

Alhaji Tukur Ahmed Jikamshin a tattaunawar mu da shi, ya bayyana cewar ko kusa ba a nuna adalci ba a zaben, don haka su, a wurinsu ba a yi zaben fidda gwanin takara ba na jam'iyyar ta PDP a Katsina

Karin bayani