'Yan hamayya na so a tsige Shema

Gwamna Shema na jihar Katsina Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gwamna Shema na jihar Katsina

'Yan jam'iyyun hamayya a jihar Katsina da ke Najeriya na so 'yan majalisar dokokin jihar su tsige gwamna Ibrahim Shema saboda ya kwatanta su da kyankyasai wadanda a cewarsa, babu abin da ya dace da su illa bugewa.

Gwamna Shema dai ya musanta cewa mkalaman nasa na tayar da hankali ne.

Sai dai 'yan hamyyar sun ce sun aikewa majalisar dokokin jihar wata takarda da ke bukatar a tsige gwamnan, suna masu cewa kalaman nasa sun sabawa rantsuwar da ya yi ta kare kundin tsarin mulkin Najeriya.

Sun kara da cewa sun aike da irin wannan takarda ga ofisoshin jakadancin Amurka da Burtaniya domin su tsoma baki a cikin lamarin.

Sai dai wani dan majalisar dokokin jihar ya ce ba su da labarin aikewa da takardar, yana mai cewa majalisar tana yin hutun mako uku domin haka ba zai ce komai ba.

Karin bayani