Wagegen gibi tsakanin Talaka da mai kudi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An samu wagegen gibin ne a mafi yawan kasashen da suka samu ci gaba na duniya

Kungiyar hadin kai da tattalin arziki a Turai, OECD ta bukaci kasashen duniya su yi hobbasa wajen rage wagegen gibin da ke tsakanin masu arziki da kuma talakawa a cikin al'umma.

Kungiyar ta ce a yanzu wagegen gibin ya kai kokoluwa a cikin shekaru 30 kuma hakan na illa ga bunkasar tattalin arziki.

A cewar OECD abin da mutanen da suka fi wadata, wadanda kuma su ne kashi goma cikin dari na al'ummar duniya ke samu, ya ninka abin da talakawa ke samu sau tara da rabi.

Hakan dai in ji kungiyar na kawo cikas ga ilmantar da talakawa tare da hana karin wadata a rayuwar al'umma, sannan kuma gibin naa karan tsaye ga sana'oi masu muhimmanci ga habakar tattalin arziki.