Mutuwa sanadiyar malariya ta ragu

Hakkin mallakar hoto GETTY IMAGES
Image caption Hukumar ta yi gargadin cewa za a iya fuskantar kalubale game da shawo kan cutar a kasashen da ke fama da cutar ebola.

Hukumar lafiya ta duniya ta ce mutanen da ke mutuwa sanadiyar kamuwa da zazzabin cizon sauro sun ragu da kimanin rabi tun daga farkon karnin da muke ciki.

A wani rahoto da hukumar ta fitar, ta kara da cewa kaimin da kasashen duniya suka kara a yunkurin kawar da cutar ya sa mutane fiye da miliyan hudu sun tsira daga kamuwa da ita.

A cewar hukumar, akasarin mutanen kananan yara ne da ke kasa da shekaru biyar da nahiyar Africa.

Hukumar ta lafiya ta ce kudaden da aka kara wajen sayen gidan sauron da ke da maganin cutar da kuma gwajin da ake yi wa masu dauke da ita cikin gaggawa da ba su magani sun taimaka wajen rage yaduwarta.

Sai dai hukumar ta yi gargadin cewa za a iya fuskantar kalubale game da shawo kan cutar musamman a kasashen da ke fama da cutar ebola.