Babu tabbacin wadatar abinci a Afrika

Yankin Sahel na Afrika
Image caption Yankin Sahel na Afrika

Wani rahoto ya nuna cewar halin ko in kula da aka nuna kan lafiyar kasa a nahiyar Afrika zai jefa nahiyar cikin wani dogon yanayi na karancin abinci.

Rahoton da kwamitin Montpellier ya bayar yace akwai bukatar dake akwai ga kungiyoyin bayar da agaji su bayar da matukar muhimmanci ga kokarin warware wannan matsalar.

Rahoton ya kara da cewar, lalacewar yanayin kasar kuma har ila yau yana tauye cigaban tattalin arziki saboda manoma na hasarar biliyoyin daloli daga amfanin gonar da suke sayarwa.

An buga rahoton ne gabanin ranar nazarin kasa ta duniya ta shekara ta 2015.

Kwamitin na Montpellier wanda ya kunshi masana ayyukan gona da harkokin kasuwanci da yanayin kasa daga Turai da Afrika - ya yi kashedin cewa watsi da halin da yanayin kasa yake ciki yana rage albarkar da ta kunsa abinda zai haddasa samun karancin yabanya da karuwar hayaki dake kawo dumamar yanayi.

Ya yi nunin cewa a Afrika illolin a bayyane suke saboda akwai shaidar da ta nuna an rigaya an lalata kashi 65 na filayen noma, kashi 30 na wuraren kiwo da kuma sare itatuwa kashi 20 bisa dari.

Jagoran kwamitin Sir Farfesa Gordon Conway daga Imperial College London ya gaya ma sashen labarai na BBC cewar "muna bata lokaci mai tsawo muna magana a kan tsirrai, muna kuma bata lokaci mai tsawo muna magana a kan dabbobi. Muna doguwar muhawara a kan ayyukan gona, to amma muna mantawa da cewar dukkan wadannan sun dogara ne da yanayin kasa."

Ya kara da cewa, gwajin na baya-bayan nan da aka yi ya nuna cewar an yi matukar watsi da yanayin kasa a nahiyar.

Yace, watsin da aka yi da yanayin kasa a nahiyar Afrika ya shafi kusan daya bisa ukku na filaye a nahiyar, yace wannan yanki ne mai girman gaske.

"akwai mutane kimanin miliyan dari da 80 da suka dogara a kan filayen da ta wani bangare an yi watsi da lafiyarsu.

Ya bayyana cewar wannan matsalar tana barazana ga harkoki na noman abinci a yankin da tuni ke fama da karancin albarkatun noma.

Karin bayani