Wakilan jam'iyyar APC na zabe

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban APC na kasa, Cif John Oyegun

Wakilan Babbar jam'iyyar adawa a Nigeria-APC na ci gaba da kada kuri'unsu domin zabar mutumin da zai yiwa jam'iyar takara a zaben Shugaban Kasa a watan Fabarairu na badi.

Ana ganin cewar takarar za ta fi zafi ne tsakanin tsohon Shugaban kasar na mulkin soja, Muhammadu Buhari da kuma tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar.

Mutane biyar ne ke takara a jam'iyyar ta APC a wannan lokacin da Nigeria ke fuskantar matsalar tabarbarewar tsaro.

Sauran 'yan takarar su ne; Rabiu Musa Kwankwaso da Rochas Okorocha da kuma Sam Nda Isaiah.

Wakilai 8,000 daga sassa daban daban na Nigeria ne ke halartar taron a babban filin wasa na Teslim Balogun da ke birnin Lagos.

Ana saran sannin sakamakon zaben fitar da gwanin a ranar Alhamis.

A ranar 14 ga watan Fabarairu ne za a gudanar da zaben shugaban kasa a Nigeria.