An daure mai tona asirin Apple

Hakkin mallakar hoto Getty

An yankewa wani tsohon jami'in kamfanin Apple wanda ya samu miliyoyin kudade ta hanyar sayarda bayanai game da kamfanin ga abokan huldar kamfanin, hukuncin daurin shekara guda a gidan yari.

Dole ne kuma Paul Shin Devine ya biya kusan $4.5 na irin kudaden da ya samu.

Abokanan hulda suna biyan Devine kudade domin ya gano musu irin kayayyakin da Apple din zai samar da kuma ayyukansa, domin hakan zai taimaka musu wajen kulla kasuwanci da kamfanin.

An kuma yankewa Devine hukuncin fiye da shekaru uku a California bayan da ya amsa laifin zarge- zargen da ake masa da suke da alaka da zamba da makarkashiya da kuma halarta kudaden haram.

Devine shi ne manajan Kamfanin Apple mai kula da samar da kaya daga shekarar 2005 zuwa 2010 a lokacin da aka tsare shi.

Tsohon jami'in ya kirkiri wani kamfani da ake kira CPK Engineering inda yake zuba tsabar kudin da ya ke karba daga abokan hulda.

An soma bincike ne akan halayyarsa bayan da aka gano wasu sakonnin email wadanda a cikinsu ya amince ya mika wasu bayanai idan an biya shi.