Amurka ta rufe gidan yarin Bagram a Afghanistan

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An bude gidan yarin Bagram tun bayan harin 11 ga watan Satumba

Ma'aikatarTsaron Amurka ta bada sanarwar rufe cibiyar tsare mutane ta karshe dake kasar Afghanistan.

Wani mai magana da yawun Pentagon ya fadawa BBC cewa dukkanin fursunonin da ake tsare dasu cikin wannan cibiya wacce ke sansanin Bagram, a yanzu imma dai an maida su wurin da ake tsare mutane na Afganistan, ko kuma an tusa keyarsu zuwa kasashensu.

Ya ce gwamnatin Kabul a yanzu itake da alhakin tsare fursunoni a Afganistan.

Bagram na daya daga cikin wuraren da rahotan majalisar dattawan Amurka ya ce jami'an CIA na amfani da hanyoyin azabtarwa wajen binciken masu laifi.

An kafa kurkukun Bagram ne jim kadan bayan harin 11 ga watan Satumba, kuma daruruwan mutanen da ake zargi ne, ke garkame a cikinsa